Wahayin Ezekiyel game da haikali ya ƙarfafa Isra’ilawan da suke Babila domin ya sa sun kasance da bege cewa za a maido da bauta ta gaskiya. A zamaninmu, an ɗaukaka bauta ta gaskiya “bisa kan tuddai” kuma muna cikin waɗanda suke gangarowa wurinta. (Ish 2:⁠2) Kana bimbini a kan gatan da kake da shi na koya game da Jehobah da kuma bauta masa?

ALBARKAR DA MUKE SAMU DON BAUTA TA GASKIYA:

  • Muna da tanadodin da suke sa mu san amsoshin muhimman tambayoyi na rayuwa, da ƙa’idodin da ya kamata mu bi, kuma suna sa mu kasance da bege.​—Ish 48:​17, 18; 65:13; Ro 15:4

  • Muna da ’yan’uwa masu ƙauna a faɗin duniya.​—Za 133:1; Yoh 13:35

  • Muna da gatan yin wa’azin bishara.​—A. M. 20:35; 1Ko 3:9

  • Muna da ‘salama ta Allah’ wadda take taimaka mana mu jimre da wahala.​—Fib 4:6, 7

  • Muna da lamiri mai kyau.​—2Ti 1:3

  • Muna da dangantaka mai kyau da Jehobah.​—Za 25:14

A waɗanne hanyoyi ne zan nuna cewa ina son bauta ta gaskiya?