•  Waƙa ta 26 da Addu’a

 • Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

 • An Maido da Bauta ta Gaskiya!”: (minti 10)

  • Eze 43:10-12​—An saukar wa Ezekiyel wahayi game da haikali ne don ya sa Yahudawa su tuba, kuma ya tabbatar musu da cewa za a maido da bauta ta gaskiya (w99 3/1 14 sakin layi na 3; it-2-E 1082 sakin layi na 2)

  • Eze 44:23​—Firistoci za su koya wa mutanen bambancin da ke tsakanin abu “mai-tsabta da marar-tsabta”

  • Eze 45:16​—Mutanen za su bi ja-gorancin waɗanda Jehobah ya naɗa (w99 3/1 16 sakin layi na 10)

 • Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)

  • Eze 43:8, 9​—Ta yaya Isra’ilawa suka ɓata sunan Allah? (it-2-E 467 sakin layi na 4)

  • Eze 45:9, 10​—Mene ne Jehobah yake bukata daga wurin waɗanda suke so su sami amincewarsa? (it-2-E 140)

  • Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?

  • Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?

 • Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Eze 44:​1-9

KA YI WA’AZI DA ƘWAZO

 • Ka Shirya Gabatarwa na Wannan Watan: (minti 15) Tattauna “Gabatarwa” na wannan watan. Ka saka bidiyon gabatarwar mujallu, sai ka tattauna wasu abubuwa a ciki.

RAYUWAR KIRISTA