Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Shaidu a ƙasar Malawi suna nuna wa juna ƙauna

LITTAFIN TARO DON RAYUWA TA KIRISTA DA HIDIMARMU Oktoba 2018

Yadda Za Mu Yi Wa’azi

Jerin tattaunawa game da dalilin da ya sa muke shan wahala da kuma abin da Allah zai yi game da hakan.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Yesu Yana Kula da Tumakinsa

Yesu makiyayi Mai Kyau, ya san bukatun kowane tumakinsa da kasawarsa da kuma karfinsa.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Ku Zama Masu Tausayi Kamar Yesu

Ta yaya Yesu ya nuna cewa shi mai tausayi ne sosai?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

“Na Nuna Muku Misali”

Yesu ya koya wa almajiransa darasi a kan kasancewa da saukin kai da kuma yi wa ’yan’uwansu hidima.

RAYUWAR KIRISTA

Kauna Ce Alamar Kiristoci na Gaskiya​—Ku Guji Son Kai da Saurin Fushi

Yesu ya ce kauna ce za ta sa a san mabiyansa na gaskiya. Idan muna so mu kaunaci ’yan’uwanmu kamar yadda Kristi ya yi, dole ne mu yi abin da zai faranta musu rai kuma mu guji yin fushi a kowane lokaci.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

“Ku ba Na Duniya ba Ne”

Mabiyan Yesu suna bukatar su kasance da karfin hali don su iya yin nasara da duniya.

RAYUWAR KIRISTA

Kauna Ce Alamar Kiristoci na Gaskiya​—Kada Ka Bata Hadin Kai da Muke Mora

Idan muna so mu ci gaba da kasancewa da hadin kai, wajibi ne mu kaunaci ’yan’uwanmu.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Yesu Ya Ba da Shaida ga Gaskiya

A matsayinmu na mabiyan Yesu, mu ma za mu ba da shaida ga gaskiya a furucinmu da kuma ayyukanmu.

RAYUWAR KIRISTA

Kauna Ce Alamar Kiristoci na Gaskiya​—Ku Yi Murna da Gaskiya

Wajibi ne mu rika murna da gaskiya da fadin gaskiya da kuma yin abubuwan da suke da kyau duk da cewa muna rayuwa a duniyar da ba a yin hakan.