Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

 RAYUWAR KIRISTA

Kana Yin Amfani da Katin JW.ORG Yadda Ya Dace Kuwa?

Kana Yin Amfani da Katin JW.ORG Yadda Ya Dace Kuwa?

Da yake muna gab da ƙunci mai girma, ya kamata mu yi wa’azi da ƙwazo. (Mis 24:11, 12, 20) Za mu iya yin amfani da katin jw.org don mu taimaka wa mutane su karanta Kalmar Allah. Katin na ɗauke da wata alama da za a iya yin scan don a ga bidiyon nan Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki? da kuma yadda za a sami ƙarin bayani ko soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Wasu mutane ba sa karɓan mujallunmu amma suna son su shiga dandalinmu. Kada mu ɓata lokaci wajen ba su katin jw.org. Amma bai kamata mu ba mutanen da ba sa son saƙonmu katin ba.

Yayin da muke sha’aninmu na yau da kullum, muna iya soma tattaunawa da mutane ta wajen ce musu: “Zan so in ba ka wani abu. Wannan katin zai kai ka dandalinmu da ke ɗauke da bayanai da kuma bidiyoyin da suka tattauna batutuwa da yawa.” (Yoh 4:7) Da yake katin jw.org bai da girma, za ka iya ɗaukansa da ɗan yawa don ka ba mutane sa’ad da ka sami damar yin hakan.