Kalami mai ratsa zuciya yana ƙarfafa ’yan’uwa a ikilisiya. (Ro 14:19) Kuma mutanen da suka yi kalamin suna samun ƙarfafa. (Mis 15:23, 28) Saboda haka, ya kamata mu riƙa kalami a ƙalla sau ɗaya a kowane taro. Hakika, ba a kowane lokaci ba ne za a riƙa kiranmu mu yi kalami ba. Don haka, zai dace mu shirya kalamai da yawa a kowane taro.

Kalami mai ratsa zuciya . . .

  • gajere ne kuma yana da sauƙin fahimta. A yawancin lokuta, ana iya yinsa a sakan 30 ko ƙasa da hakan

  • daga zuciya ake yi ba karatu ba

  • ba maimaita kalamin da wani ya yi ba ne

Idan kai aka fara kira, . . .

  • ka ba da amsa mai sauƙi kuma kai tsaye

Idan wani ya riga ya ba da amsar, za ka iya . . .

  • bayyana nassin da ya goyi bayan amsar da aka bayar

  • faɗin yadda batun ya shafe mu

  • bayyana yadda za mu yi amfani da darasin

  • ba da wani labarin da ya bayyana darasin da kyau