2:1-8, 14, 37, 38, 41-47

Yawancin Yahudawa da suka zo Urushalima a lokacin Fentakos na shekara ta 33 bayan mutuwar Yesu, sun zo ne daga wasu ƙasashe. (A. M 2:​9-11) Duk da cewa suna bin Dokar da Aka Bayar ta Hannun Musa, da alama a ƙasashen waje aka haife su har suka girma. (Irm 44:1) Don haka, kamanin wasu daga cikinsu da yadda suke magana ya yi dabam da na Yahudawa. Da mutane 3,000 daga ƙasashe dabam-dabam suka yi baftisma, ikilisiyar Kirista ta ƙunshi mutane daga al’adu dabam-dabam. Duk da cewa al’adunsu sun bambanta, sukan je “Haikali da nufi ɗaya.”​—A. M 2:46.

Ta yaya za ka nuna cewa ka damu da . . .

  • mutanen da suka fito daga wasu ƙasashe da suke zama a yakinku?

  • ’yan’uwa maza da mata da suka fito daga wasu ƙasashe a ikilisiyarku?