Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafin Taro Don Rayuwa Ta Kirista da Hidimarmu  |  Nuwamba 2017

 RAYUWAR KIRISTA

Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Komawa Ziyara

Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Komawa Ziyara

ME YA SA YAKE DA MUHIMMANCI: Yawancin mutanen da suke saurarar wa’azinmu sun daɗe suna son su san gaskiya game da Allah. (Ish 55:6) Don mu taimaka musu su san gaskiyar, wajibi ne mu riƙa komawa a kai a kai. Ƙalubalen da mutane suke fuskanta ya bambanta. Don haka, yadda za mu taimaka musu ba zai zama iri ɗaya ba. Duk da haka, nazarin zai yi tasiri sosai idan muka shirya da kyau da kuma tsara abubuwan da za mu tattauna a kowace ziyara. Mu kuma kafa maƙasudin soma nazarin Littafi Mai Tsarki da maigidan.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Ka koma da wuri, wataƙila bayan kwanaki kaɗan.​—Mt 13:19

  • Ka daraja maigidan kuma ka mai da shi abokinka. Ka saki jiki a gidan

  • Ka fara da gaisuwa. Ka kira shi da sunansa. Ka tuna masa dalilin da ya sa ka dawo, wataƙila don ka amsa wata tambaya ko don ka ba shi sabuwar mujalla, ko don ka nuna masa dandalinmu, ko bidiyo ko kuma ka nuna masa yadda muke nazari da mutane. Ka canja batun da kuke tattaunawa idan maigidan ya zaɓi wani batu dabam.​—Fib 2:4

  • Ka taimaka masa ya so gaskiya ta wajen karanta masa wani Nassi ko kuma ka ba shi wata mujalla. (1Ko 3:6) Ka kasance da dangantaka mai kyau da shi

  • Ka yi shiri don ziyara ta gaba