Littafin Yunana ya nuna mana cewa Jehobah ba zai yashe mu ba idan muka yi kuskure. Amma Jehobah yana bukatar mu koyi darasi daga kuskuren da muka yi, kuma mu yi canjin da ake bukata.

Yun 1:3

Wane kuskure ne Yunana ya yi yayin da Jehobah ya ba shi aiki?

Yun 2:​1-10

Mene ne Yunana ya yi addu’a a kai, kuma ta yaya Jehobah ya amsa addu’arsa?

Yun 3:​1-3

Ta yaya Yunana ya nuna cewa ya koyi darasi daga kuskurensa?