Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafin Taro Don Rayuwa Ta Kirista da Hidimarmu  |  Nuwamba 2017

 RAYUWAR KIRISTA

Darussa Daga Littafin Yunana

Darussa Daga Littafin Yunana

A cikin Littafi Mai Tsarki, Jehobah ya sa an rubuta labaran maza da mata masu aminci don mu iya koyan darasi daga labaransu. (Ro 15:4) Mene ne ka koya daga littafin Yunana? Ku kalli bidiyon nan Ibada Ta Iyali: Yunana​—Ya Koyi Rahama Daga Jehobah, sai ku amsa tambayoyin nan:

  • Waɗanne ƙalubale ne masu shelar nan uku suka fuskanta a bidiyon?

  • Ta yaya littafin Yunana zai iya ƙarfafa mu idan aka yi mana horo ko kuma muka rasa wata gata a ikilisiya? (1Sam 16:7; Yun 3:​1, 2)

  • Ta yaya labarin Yunana zai taimaka mana mu kasance da ra’ayin da ya dace game da mutanen da ke yankin da muke wa’azi? (Yun 4:11; Mt 5:7))

  • Ta yaya abin da ya faru da Yunana zai ƙarfafa mu sa’ad da muke rashin lafiya mai tsanani? (Yun 2:​1, 2, 7, 9)

  • Mene ne wannan bidiyon ya koya maka game da muhimmancin karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin bimbini?