HASUMIYAR TSARO

Tambaya: Wane ne ya fi ba da kyauta a sama da duniya?

Nassi: Yaƙ 1:17

Littafi: Wannan mujallar ta yi magana a kan yadda za mu nuna godiya don kyauta mafi daraja da Allah ya ba mu.

KU KOYAR DA GASKIYA

Tambaya: Mene ne sunan Allah?

Nassi: Za 83:⁠18

Gaskiya: Sunan Allah shi ne Jehobah.

YADDA IYALINKU ZA TA ZAUNA LAFIYA

Gabatarwa: Muna nuna wa mutane wannan bidiyon game da iyali. [Ka nuna bidiyon Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya.]

Littafi: Idan kana son ka karanta ƙasidar da aka ambata a bidiyon nan, zan iya ba ka shi ko kuma in nuna maka yadda za ka sauƙar da shi a dandalinmu.

KA RUBUTA TAKA GABATARWA

Ku yi amfani da fasalin da ke baya don rubuta taku gabatarwar wa’azi.