Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Ana ba da ƙasidar nan Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya a ƙasar Georgia

LITTAFIN TARO DON RAYUWA TA KIRISTA DA HIDIMARMU Nuwamba 2017

Gabatarwa

Yadda za a iya ba da hasumiyar tsaro da kuma koya wa mutane gaskiya game da sunan Allah. Ka yi amfani da misalan nan don ka rubuta taka gabatarwar.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

“Ku Bidi Jehobah, Kuma Za Ku Rayu”

Mene ne bidan Jehobah yake nufi? Mene ne za mu iya koya daga labarin Isra’ilawa da suka ki bidan Jehobah?

RAYUWAR KIRISTA

Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Komawa Ziyara

Ta yaya za ka yi koma ziyara mai kayatarwa? Ka sa su so wa’azin da kake yi, ka tsara abubuwan da za ku tattauna, ka kasance da makasudi.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Ka Koyi Darasi Daga Kurakurenka

Labarin Yunana ya nuna cewa Jehobah ba ya gajiya da mu sa’ad da muka yi kuskure, amma yana so mu koyi darasi daga kuskuren.

RAYUWAR KIRISTA

Darussa Daga Littafin Yunana

Nazari tare da bimbini a kan labarin Yunana zai taimaka mana mu jimre idan ba mu sami abin da muke sa ran cewa za mu samu ba da taimaka mana mu kasance da ra’ayi mai kyau game da wa’azi da muke yi. Har ila, zai taimaka mana mu gaya wa Allah damuwanmu.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Mene ne Jehobah Yake Bukata Daga Gare Mu?

Mene ne alakar da ke tsakanin ibadarmu da dangantarkarmu da ’yan’uwa?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Ka Yi Tsaro da Kuma Kwazo a Hidimarka ga Jehobah

Mutane suna ganin kamar ba zai taba yiwu Babiloniyawa su halaka Urushalima ba. Duk da haka, wannan annabcin zai faru kuma Habakkuk yana bukatar ya yi tsaro kuma ya yi kwazo a hidimarsa.

RAYUWAR KIRISTA

Ka Ci gaba da Kwazo a Ibadarka Ko da Yanayinka Ya Canja

Mene ne zai taimaka mana mu ci gaba da kwazo a hidimar Jehobah duk wasu canjin yanayin da muke fuskata a rayuwa?