Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafin Taro Don Rayuwa Ta Kirista da Hidimarmu  |  Nuwamba 2016

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MISALAI 27-31

Yadda Littafi Mai Tsarki Ya Kwatanta Matar Kirki

Yadda Littafi Mai Tsarki Ya Kwatanta Matar Kirki

Misalai sura 31 yana ɗauke da saƙo mai muhimmanci da mahaifiyar Sarki Lemuel ta aika masa. Shawarar da ta ba shi ta koya masa yadda zai gane macen kirki.

Macen kirki tana da riƙon amana

31:10-12

  • Tana ba da shawara mai kyau a iyali kuma tana ladabi da biyayya

  • Maigidanta yana barin ta ta tsai da wasu shawara ba tare da cewa sai lallai ta nemi izininsa ba

Macen kirki tana da ƙwazo

31:13-27

  • Ta san yadda za ta kashe kuɗi don iyalinta su riƙa saka tufa mai kyau kuma su ci abinci mai gina jiki

  • Tana aiki da ƙwazo kuma tana kula da iyalinta dare da rana

Macen kirki tana ƙaunar Allah

31:30

  • Tana tsoron Allah kuma tana da dangantaka mai kyau da shi