Halin macen kirki yana sa a daraja mijinta. A zamanin Sarki Lemuel, mutumin da ya auri macen kirki “sananne ne a ƙofofin gari.” (Mis 31:23) A yau, ana iya naɗa mazan kirki su yi hidima a matsayin dattawa da bayi masu hidima. Idan suna da aure, halin matansu zai sa a ga ko sun cancanci su yi hidima ko a’a. (1Ti 3:4, 11) Mazan da suka auri matan kirki suna daraja su. Ban da haka ma, ikilisiya tana ɗaukan matan da daraja.

Macen kirki tana taimaka wa mijinta ya yi hidima ta wajen . . .

  • ƙarfafa shi da kalamai masu daɗi.—Mis 31:26

  • barin shi ya riƙa taimaka wa ‘yan’uwa a ikilisiya.—1Ta 2:7, 8

  • kasancewa da sauƙin kai.—1Ti 6:8

  • ƙin yin bincike a kan batutuwan sirri na ikilisiya.—1Ti 2:11, 12; 1Bi 4:15