HASUMIYAR TSARO

Tambaya: Yaya za ka kwatanta sama idan wani ya ce ka yi hakan?

Nassi: Yoh 8:23

Abin da Za Ka Ce: Wannan talifin Hasumiyar Tsaro ya tattauna yadda Yesu da Ubansa suka kwatanta sama.

KU KOYAR DA GASKIYA

Tambaya: Shin ka yarda cewa wannan annabcin Littafi Mai Tsarki yana kwatanta abin da yake faruwa a yau?

Nassi: 2Ti 3:1-5

Gaskiya: Da yake annabcin Littafi Mai Tsarki game da kwanaki na ƙarshe yana cika a yau, muna da tabbaci cewa annabcin da aka yi game da aljanna zai cika.

ME YA SA ZAI DACE MU YI NAZARIN LITTAFI MAI TSARKI? (Bidiyo)

Gabatarwa: Muna nuna wa mutane wani gajeren bidiyo da ya tattauna yadda za mu sami amsoshi masu gamsarwa ga tambayoyi masu muhimmanci na rayuwa. [Ka nuna masa bidiyon.]

Abin da Za Ka Ce: Wannan littafin ya tattauna yadda Allah zai magance matsalolin duniya. [Ka ba da Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ko kuma Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?

KA RUBUTA TAKA GABATARWA

Ku yi amfani da fasalin da ke baya don rubuta taku gabatarwar wa’azi.