• Waƙa ta 106 da Addu’a

 • Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

 • Na Tsawata Masa Fuska da Fuska”: (minti 10)

  • [Ku kalli bidiyon Gabatarwar Littafin Galatiyawa.]

  • Ga 2:​11-13​—Da Kiristoci Yahudawa suka ziyarci Bitrus, sai ya daina sha’ani da Kiristocin da ba Yahudawa ba don yana tsoron Kiristoci Yahudawa (w17.04 27 sakin layi na 16)

  • Ga 2:14​—Bulus ya gargaɗi Bitrus (w13 3/15 5 sakin layi na 12)

 • Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)

  • Ga 2:20b​—Yaya ya kamata mu riƙa ɗaukar fansar Yesu kuma me ya sa? (w14 9/15 16 sakin layi na 20-21)

  • Ga 3:1a​—Me ya sa Bulus ya ce Galatiyawa suna “hauka”? (mwbr19.05-HA an ɗauko daga it-1 880)

  • Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?

  • Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?

 • Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Ga 2:​11-21 (th darasi na 10)

KA YI WA’AZI DA ƘWAZO

RAYUWAR KIRISTA

 • Waƙa ta 92

 • Yadda Kowanenmu Zai Kula da Wuraren Ibadarmu”: (minti 15) Tattaunawar da dattijo zai yi. Bayan kun kalli bidiyon nan Ku Riƙa Kula da Wuraren Ibadarmu kuma kun amsa tambayoyin, ka ɗan gana da ɗan’uwan da ke wakiltar ikilisiyarku a kwamitin da ke kula da Majami’ar Mulki ta wajen yi masa tambayoyin nan (Idan ba ku da wakili a ikilisiyarku, ka gana da mai tsara ayyukan rukunin dattawa. Ka gana da mai kula da gyare-gyare idan ikilisiyarku ce kaɗai take amfani da Majami’ar Mulkin.) Shin muna kula da Majami’ar Mulki a kai a kai yadda ya kamata? Muna ɗaukan matakan kāriya sa’ad da muke aikin kuwa? Waɗanne ayyuka ne muka yi a Majami’ar Mulkinmu kuma mene ne muke so mu yi a nan gaba? Idan wani yana da aikin hannu ko yana so ya koya, mene ne zai yi? Ta yaya kowannenmu zai iya taimaka wajen kula da Majami’ar Mulki?

 • Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) bhs babi na 8 sakin layi na 11-21 da Ƙarin Bayani na 10 da 21

 • Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)

 • Waƙa ta 72 da Addu’a