Kamar yadda Kiristoci a ƙarni na farko suka taimaka wa ’yan’uwa masu bi da bala’i ya shafa, mu ma a yau za mu iya yin hakan. (Yoh 13:​34, 35) Ku kalli bidiyon nan Yadda Muka Nuna Ƙauna ta Wajen Kai Agaji a Karibiya don ku ga yadda ’yan’uwa suka taimaka ma Shaidu da bala’i ya shafa a Karibiya. Bayan haka, ku amsa tambayoyin nan:

  • Ta yaya guguwa da aka yi a Karibiya ta shafi ’yan’uwanmu?

  • Ta yaya Jehobah ya yi amfani da ’yan’uwa maza da mata don ya taimaka wa ’yan’uwanmu da ke Karibiya?

  • Ta yaya waɗanda guguwa ta shafa suka amfana daga taimakon da ’yan’uwanmu suka ba su?

  • ’Yan’uwa guda nawa ne suka yi aikin agaji a Karibiya?

  • Ta yaya kowannenmu zai iya taimakawa a aikin agaji?

  • Da ka kalli bidiyon nan, yaya ka ji game da kasancewa cikin wannan ƙungiyar?