45:2-5

Da alama cewa Baruch mai ilimi ne kuma shi ma’aikaci ne a fādar sarki. Ko da yake yana bauta wa Jehobah kuma ya taimaka wa Irmiya, amma akwai lokacin da ya soma bijirewa. Ya soma ‘biɗa wa kansa manyan abu,’ wataƙila ƙarin matsayi a fādar sarki ko kuma kayan duniya. Yana bukatar ya yi gyara don ya tsira sa’ad da aka halaka Urushalima.