Zadakiya ya ƙi bin umurnin da Jehobah ya ba shi cewa ya miƙa wuya ga Babila

39:4-7

  • An kashe yaran Zadakiya a idonsa. Shi kuma an ɗaure shi da sarƙa kuma an saka shi a kurkuku har mutuwarsa a Babila

Ebed-melek ya dogara ga Jehobah kuma ya taimaka wa Irmiya

39:15-18

  • Jehobah ya yi alkawari cewa zai kāre Ebed-melek a lokacin da za a halaka mutanen Yahuda

Kafin a halaka Urushalima, Irmiya ya yi shekaru da yawa yana wa’azi da gaba gaɗi

40:1-6

  • Jehobah ya kāre Irmiya a lokacin da aka halaka Urushalima kuma ya sa Babiloniyawa su saki Irmiya