Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafin Taro Don Rayuwa Ta Kirista da Hidimarmu  |  Mayu 2016

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ZABURA 1-10

Daraja Yesu Zai Sa Mu Kasance da Salama da Jehobah

Daraja Yesu Zai Sa Mu Kasance da Salama da Jehobah

An annabta cewa za a yi hamayya da Jehobah da kuma Yesu

2:1-3

  • An annabta cewa al’ummai ba za su amince da ikon Yesu ba, a maimakon haka, za su nace a kan nasu

  • Wannan annabcin ya cika a zamanin Yesu kuma yana cika sosai a yau

  • Marubucin zabura ya ce al’ummai za su riƙa gunagunin banza kuma hakan yana nufin cewa ba za su yi nasara ba

Waɗanda suke daraja Sarkin da Jehobah ya naɗa ne kaɗai za su sami rai

2:8-12

  • Za a halaka dukan mutanen da ke hamayya da Yesu

  • Mutane za su sami mafaka da salama idan suka daraja Yesu