MUHIMMANCINSA: Littafin 1 Korintiyawa yana cikin wasiƙu guda 14 da manzo Bulus ya rubuta don ya ƙarfafa ’yan’uwansa Kiristoci. Mai rubuta wasiƙa yakan zaɓi furucin da zai yi amfani da shi don ya san cewa wanda zai karɓi wasiƙar zai riƙa karanta ta a kai a kai. Rubuta wasiƙa hanya ce mai kyau ta yi wa ’yan’uwa da abokan arziki wa’azi. Ban da haka ma, za a iya yin amfani da wasiƙu wajen yin wa’azi ga mutanen da ba ma samunsu a gida. Alal misali, wataƙila wani ya so saƙonmu amma ba a yawan samun sa a gida. Wasu a yankinmu suna da jami’an tsaro da suke gadi a gidajensu ko suna da manyan ƙofofin da ba a cika barin mutane su shiga. Ƙari ga haka, wasu suna zama a wuraren da ke bayan gari inda mutane ba sa cika zuwa. Waɗanne abubuwa ne ya kamata mu tuna da su sa’ad da muke rubuta wasiƙa ga wani da ba mu taɓa haɗuwa da shi ba?

YADDA ZA MU YI HAKAN:

  • Ka rubuta abin da za ka iya faɗa a gabansa. Ka gabatar da kanka a farkon wasiƙar kuma ka nuna dalilin da ya sa kake rubuta wasiƙar. Za ka iya yin wata tambaya a wasiƙar kuma ka ce mutumin ya shiga dandalinmu don ya sami amsar. Ka gaya masa game da darussa da muke koya daga Littafi Mai Tsarki a dandalinmu, kuma ka nuna masa tsarin da muke da shi na nazarin Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, ka ambata wasu jigo da ke littattafan da muke nazari da su. Za ka iya saka littattafanmu kamar su katin da ya bayyana yadda za a shiga dandalinmu ko takardar gayyata ko kuma warƙa a cikin wasiƙar

  • Kada ka yi dogon jawabi. Wasiƙar ta zama gajeriya don kada wadda ka rubuta masa ya gaji da karatu.​—Ka duba samfurin wasiƙa a shafi na 8

  • Ka sake karanta wasiƙar don ka ga ko akwai kurakurai kuma ka tabbata cewa wasiƙar tana da daɗin karatu kuma za ta ƙarfafa mutumin in ya karanta