• Ka yi amfani da adireshinka. Idan ka ga ba zai yiwu ka ba da adireshinka ba, za ka iya ba da adireshin Majami’ar Mulkinku idan dattawa sun ba ka izinin yin hakan. Amma, KAR KA YI amfani da adireshin ofishinmu a matsayin adireshinka.

  • Ka yi amfani da sunan mutumin idan ka sani. Hakan zai sa ya san cewa shi aka rubuta ma wasiƙar.

  • Sa’ad da kake rubuta wasiƙar, ka mai da hankali ga ƙa’idodin rubutu na yaren don wasiƙar ta yi kyau. Wasiƙar ta kasance da tsabta da kuma tsari. Idan da hannu za ka rubuta, ka rubuta a hanyar da za a iya karantawa da sauƙi. Kada ka yi amfani da kalmomi masu wuyar fahimta ko kuma waɗanda ba za su daraja mai karatun ba.

Samfurin wasiƙar da ke nan ya nuna yadda za mu yi hakan. Kar ka bi wasiƙar nan kalma bayan kalma sa’ad da kake rubuta ma wani a yankinku. Sa’ad da kake rubuta wasiƙar, ka yi la’akari da manufar wasiƙar da yanayin yankinku da kuma al’adunku.