2:14-16

Dukanmu muna bukatar mu ci gaba da kyautata dangantakarmu da Allah. (Afi 4:​23, 24) Don ka samu ci gaba a ibadarka, dole ne ka riƙa nazarin Kalmar Allah da kasance da halaye masu kyau da kuma yin tunani a kan yadda za ka ƙara yawan ayyukan ibada da kake yi.

Har yanzu kana ƙaunar Jehobah kamar yadda kake ƙaunar sa shekarar da ta shige ko shekaru goma da suka shige ko kuma sa’ad da ka yi baftisma?