An tsara ƙasidar nan Su Wane Ne Suke Yin Nufin Jehobah a Yau? ne don a riƙa amfani da ita wajen tattaunawa da ɗalibai kafin a soma nazari da su kowane mako ko kuma bayan an kammala. * Darasi na 1 zuwa 4 zai sa ɗaliban su san mu. Darasi na 5 zuwa 14 zai taimaka musu su san ayyukanmu. Darasi na 15 zuwa 28 kuma zai nuna musu abubuwa da ƙungiyarmu take cim ma. Zai fi kyau a tattauna darussan daga farko zuwa ƙarshe, sai dai idan ɗalibin yana so a tattauna wani darasi na ƙasidar. Kowane darasi shafi ɗaya ne kuma za a iya tattauna shi cikin minti biyar zuwa goma.

  • Ka sa ɗalibin ya mai da hankali ga tambaya wadda ita ce jigon darasin

  • Za ku iya karanta darasin gabaki ɗaya ko sakin layi bayan sakin layi

  • Ku tattauna abin da kuka karanta. Ka yi amfani da tambayoyin da ke ƙarƙashin shafin da kuma hotunan. Ku karanta nassosin da ba a yi ƙaulinsu ba da suka dace kuma ku tattauna su. Ka nuna cewa kan maganar ta amsa tambaya wadda ita ce jigon darasin

  • Idan akwai akwatin nan “Ka Ƙara Bincike,” ku karanta shi tare kuma ka ƙarfafa ɗalibin ya bi shawarar da aka bayar a ciki

^ sakin layi na 3 Ƙasidar da ke dandalinmu ce ta kwana-kwanan nan.