Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

 RAYUWAR KIRISTA

Fansar Yesu Ta Sa Ya Yiwu a Ta da Matattu

Fansar Yesu Ta Sa Ya Yiwu a Ta da Matattu

Taron tuna da mutuwar Yesu yana ba mu zarafin yin bimbini a kan yadda za mu amfana a nan gaba daga fansar Yesu. Ɗaya cikin amfanin shi ne tashin matattu. Ba nufin Allah ba ne mutane su riƙa mutuwa. Shi ya sa mutuwa ce abin da ta fi sa mu baƙin ciki a yau. (1Ko 15:26) Yesu ya yi baƙin ciki sosai sa’ad da ya ga almajiransa suna kuka don Li’azaru ya mutu. (Yoh 11:33-35) Tun da Yesu yana kamar Ubansa sosai, muna da tabbaci cewa Jehobah ba ya farin ciki sa’ad da ya ga muna baƙin ciki domin wani danginmu ko abokinmu ya rasu. (Yoh 14:7) Jehobah yana marmarin ta da amintattun bayinsa daga mutuwa, kuma ya kamata mu yi hakan.Ayu 14:14, 15.

Tun da Jehobah Allah ne mai tsari, muna da tabbaci cewa za a bi tsari sa’ad da ake ta da matattu. (1Ko 14:33, 40) Maimakon yin jana’iza, wataƙila za a yi liyafa don a marabci waɗanda suka tashi daga matattu. Shin kana bimbini a kan tashin matattu, musamman sa’ad da kake makoki? (2Ko 4:17, 18) Kana godiya ga Jehobah don ya yi mana tanadin fansa kuma ya bayyana mana a cikin Littafi Mai Tsarki cewa zai ta da matattu?Kol 3:15.

  • Wane abokinka ko danginka ne kake ɗokin gani ya tashi daga mutuwa?

  • Wane mutum da aka ba da labarinsa cikin Littafi Mai Tsarki ne kake son ka gani kuma ka tattauna da shi?