Da ikilisiyar da ke Roma ta ji cewa Bulus yana zuwa, wasu ’yan’uwa sun yi tafiya na wajen kilomita 64 don su marabce shi. Hakan ya ƙarfafa Bulus kuwa? Littafi Mai Tsarki ya ce, “Da Bulus ya gan su kuwa ya yi godiya ga Allah, ya kuma ƙara samun ƙarfin gwiwa.” (A. M 28:15) Ko da yake Bulus yana ƙarfafa ’yan’uwa a ikilisiyoyin da ya je, a wannan karon da aka kama shi, ’yan’uwan ne suka ƙarfafa shi.​—2Ko 13:10.

A yau, masu kula da da’ira suna zuwa ikilisiyoyi da yawa don su ƙarfafa mu. Kamar dukan bayin Jehobah, su ma a wasu lokuta suna fuskantar matsaloli kamar gajiya da damuwa da kuma sanyin giwa. Don haka, idan mai kula da da’ira da matarsa suka sake zuwa ikilisiyarku, mene ne za ka iya yi don dukanku ‘ku ƙarfafa juna’?​—Ro 1:​11, 12.

  • Ka fita wa’azi a makon da mai kula da da’ira ya zo. Mai kula da da’ira yana farin ciki sosai idan ya ga ƙoƙarin da masu shela suke yi don su fita wa’azi in ya ziyarce su. (1Ta 1:​2, 3; 2:20) Kana iya yin hidimar majagaba na ɗan lokaci a watan da zai zo. Kana iya yin wa’azi tare da shi ko matarsa ko kuma ka kai shi ko matarsa wurin ɗalibanka don ku yi nazari. Shi da matarsa suna son yin wa’azi tare da masu shela dabam-dabam har da waɗanda ba su daɗe da zama masu shela ba da kuma waɗanda suke ganin ba su iya wa’azi sosai ba.

  • Ka nuna musu karimci. Kana iya ba su wurin kwanciya ko kuma abinci. Hakan zai sa mai kula da da’irar da matarsa su fahimci cewa kana ƙaunar su. Kuma ba sai ka kashe kuɗi sosai a kan su ba.​—Lu 10:​38-42.

  • Ka yi amfani da shawarwarin da ya ba ka. Masu kula da da’ira suna taimaka mana mu bauta wa Jehobah da kyau sosai. A wasu lokuta, za su iya ja mana kunne. (1Ko 5:​1-5) Suna farin ciki sosai idan suka ga muna yin abin da suka gaya mana.​—Ibr 13:17.

  • Ka gode musu. Ka gaya wa mai kula da da’ira da matarsa yadda ka amfana daga ƙoƙarin da suke yi. Za ka iya yin haka ta wurin rubuta masa gajeren wasiƙa ko kuma ka gaya masa da baki.​—Kol 3:15.