Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafin Taro Don Rayuwa Ta Kirista da Hidimarmu  |  Janairu 2018

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 10-11

Yesu Ya Karfafa Mutane Kuma Ya Sa Sun Sami Kwanciyar Hankali

Yesu Ya Karfafa Mutane Kuma Ya Sa Sun Sami Kwanciyar Hankali

11:28-30

“Karkiyata mai-sauƙi ce”

Da yake Yesu kafinta ne, babu shakka ya san yadda ake gyara karkiya. Wataƙila ma yana amfani da fata ko wani abu sa’ad da yake gyara ta don a ji daɗin yin aiki da ita. A lokacin da muka ɗauki karkiyar Yesu sa’ad da muka yi baftisma, mun soma wani babban aiki ne mai wuya, amma idan muka ci gaba, za mu sami ƙarfafa da albarka sosai.

Waɗanne albarku ka samu tun lokacin da ka ɗauki karkiyar Yesu?