Matta sura 8 da 9 sun tattauna hidimar da Yesu ya yi a yankin Galili. A lokacin da Yesu ya warkar da mutane, ya nuna cewa yana da iko. Amma abin da ya fi muhimmanci shi ne, hakan ya nuna cewa ya ji tausayin mutane kuma ya ƙaunace su sosai.

 1. Yesu ya warkar da wani kuturu.​—Mt 8:​1-3

 2. Yesu ya warkar da bawan wani soja.​—Mt 8:​5-13

  Ya warkar da mahaifiyar Bitrus.​—Mt 8:​14, 15

  Ya fitar da aljannu kuma ya taimaka wa mutanen da suke shan wahala. ​—Mt 8:​16, 17

 3. Yesu ya fitar da mugayen aljannu kuma ya sa suka shiga cikin aladu.​—Mt 8:​28-32

 4. Yesu ya warkar da mai-ciwon inna.​—Mt 9:​1-8

  Ya warkar da wata mata da ta taɓa rigarsa kuma ya ta da ’yar Yayirus.​—Mt 9:​18-26

  Ya warkar da makaho da kuma wani bebe.​—Mt 9:​27-34

 5. Yesu ya je birane da ƙauyuka yana warkar da kowace irin cuta.​—Mt 9:​35, 36

Ta yaya zan ƙara yin ƙaunar mutanen da ke kusa da ni kuma in ji tausayinsu?