Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafin Taro Don Rayuwa Ta Kirista da Hidimarmu  |  Janairu 2018

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | MATTA 1-3

“Mulkin Sama Ya Kusa”

“Mulkin Sama Ya Kusa”

3:4

  • Tufafin Yohanna da shigarsa sun nuna cewa ya sauƙaƙa rayuwarsa don ya iya yin nufin Allah

  • Babban gatan da Yohanna ya samu na shirya wa Yesu hanya ya fi kowace irin sadaukarwa da ya yi muhimmanci

Idan muka sauƙaƙa rayuwarmu, hakan zai taimaka mana mu mai da hankali ga yin nufin Allah. Ƙari ga haka, zai sa mu yi farin ciki. Za mu iya sauƙaƙa rayuwarmu idan mun . . .

  • san ainihin bukatunmu

  • daina sayan abubuwan da ba ma bukata

  • rubuta abubuwan da muke bukata

  • kawar da abubuwan da ba ma amfani da su

  • biya bashin da ake bin mu

  • daina wasu ayyukan da suke ɗaukan lokaci sosai

Abincin Yohanna shi ne fari da zuma

Wane makasudi ne zan iya cim ma idan na sauƙaƙa rayuwata?