Yana da muhimmanci mu dogara ga Jehobah ko da a wane irin yanayi muke ciki. (Za 25:1, 2) A ƙarni na takwas kafin haihuwar Yesu, Yahudawa a birnin Yahuda sun fuskanci yanayin da ya gwada bangaskiyarsu ga Jehobah. Za mu iya koyan darussa daga abin da ya faru. (Ro 15:4) Ka nemi amsoshi ga tambayoyi na gaba, bayan ka kalli bidiyon nan ‘Ya Jehobah, . . . a Gare Ka Na Dogara.’

  1. Wane yanayi ne Hezekiya ya fuskanta?

  2. Ta yaya Hezekiya ya bi ƙa’idar da ke Misalai 22:3 sa’ad da ya lura cewa za a iya kawo musu hari?

  3. Me ya sa Hezekiya bai yi tunanin ba da kai ga Assuriyawa ko kuma ya nemi taimakon Masarawa ba?

  4. Ta yaya Hezekiya ya kafa misali mai kyau ga Kiristoci?

  5. Wane yanayi ne a yau yake gwada bangaskiyarmu ga Jehobah?

Ka rubuta yanayoyin da za ka nuna cewa kana dogara ga Jehobah.