Sarki Sennakerib na Assuriya ya tura Rabshakeh zuwa Urushalima don ya gaya musu cewa su ba da kansu. Assuriyawa sun yi amfani da dabaru dabam-dabam don su sa Yahudawa su ba da kai ba tare da sun yi yaƙi ba.

  • Ba mai taimakonku. Masarawa ba za su iya taimaka muku ba.Ish 36:6

  • Shakka. Jehobah ba zai yi yaƙi a madadinku ba domin yana fushi da ku.Ish 36:7, 10

  • Tsorata. Ba ku isa ku yi yaƙi da sojojin Assuriyawa ba.Ish 36:8, 9

  • Jarrabawa. Ba da kanku ga Assuriyawa zai inganta rayuwarku.Ish 36:16, 17

Hezekiya ya kasance da bangaskiya sosai ga Jehobah

37:1, 2, 14-20, 36

  • Ya yi iya ƙoƙarinsa don ya kāre birnin daga harin da za a kawo musu

  • Ya yi addu’a ga Jehobah ya cece su kuma ya ƙarfafa jama’a su yi hakan

  • Jehobah ya albarkace shi don bangaskiyarsa ta wajen tura mala’ika ya halaka sojojin Assuriyawa guda 185,000 a dare ɗaya