MUHIMMANCINSA:

Muna so mu sa mutanen da muka yi musu wa’azi su sami ci gaba. (1Ko 3:6) Idan muka sami wani da ke son saƙonmu, zai dace mu yi wata tambaya da za mu dawo mu tattauna da shi. Hakan zai sa mutumin ya so ka dawo kuma kai ma za ka so komawa. Idan muka koma, sai mu gaya masa cewa mun dawo ne don mu amsa tambayar da muka yi kwanan baya.

YADDA ZA MU CIM MA HAKAN:

  • Sa’ad da kake shirya abin da za ka faɗa a wa’azi, ka shirya tambayar da za ka amsa idan ka dawo. Zai iya zama wata tambaya da aka ba da amsarta a littafin da kake ba mutane. Ko kuma wata tambaya da aka ba da amsarta a ɗaya daga cikin littattafan da muke amfani da su wajen yin nazari da mutane da kake so ka nuna wa mutumin idan ka dawo.

  • Sa’ad da kake kammala tattaunawa da wani da ke son saƙonmu, ka gaya masa cewa kana so ka dawo don ku ci gaba da tattaunawar. Bayan haka, sai ka gaya masa tambayar da kake so ka dawo don ku tattauna. Ka karɓi lambarsa ko adireshinsa idan zai yiwu.

  • Idan ka gaya masa lokacin da za ka dawo, ka yi ƙoƙari ka cika alkawarinka.Mt 5:37.