Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafin Taro Don Rayuwa Ta Kirista da Hidimarmu  |  Janairu 2016

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | EZRA 1-5

Jehobah Yana Cika Alkawuransa

Jehobah Yana Cika Alkawuransa
DUBA
Kalma
Hoto

Jehobah ya ce za a dawo da bauta ta gaskiya a hankalin Urushalima. Amma bayan Isra’ilawa sun dawo daga bauta a Babila, sun fuskanci matsaloli da yawa, har da umurnin da sarki ya bayar cewa a dakatar da aikin gine-ginen. Mutane da yawa sun ji tsoro cewa ba za a taɓa kammala aikin ba.

 1. A misalin 537 K.H.Y.

  Cyrus ya ce a sake gina haikalin

 2. 3:3

  Wata na bakwai

  An shirya bagadi kuma an yi hadaya

 3. 3:10, 11

  536 K.H.Y.

  An kafa tushen

 4. 4:23, 24

  522 K.H.Y.

  Sarki Artaxerxes ya dakatar da ginin

 5. 5:1, 2

  520 K.H.Y.

  Zakariya da Haggai sun ƙarfafa mutanen su soma ginin

 6. 6:15

  515 K.H.Y.

  An kammala haikalin