1. Ka karanta tambayar da ke da lamba don ka taimaka wa maigidan ya mai da hankali ga darasin.

  2. Ka karanta sakin layi na gaba.

  3. Ka karanta nassosin da aka rubuta “karanta” kuma ka yi amfani da tambayoyi don taimaka wa maigidan ya ga yadda nassosin suka amsa tambaya da ke da lamba.

  4. Idan akwai wani sakin layi a ƙarƙashin tambayar, ka maimaita batu na 2 da 3. Idan akwai wani bidiyo a dandalin jw.org da ya yi magana a kan tambayar, ka saka wa maigidan.

  5. Don ka tabbata cewa maigidan ya fahimci batun, ka sa ya amsa tambayar da ke da lamba.