Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Gabatarwa

Gabatarwa

HASUMIYAR TSARO

Tambaya: Mutane da yawa suna daraja Littafi Mai Tsarki, amma suna tsammani cewa yana da wuyan fahimta. Mene ne ra’ayinka game da Littafi Mai Tsarki?

Nassi: Ro 15:4

Abin da Za Ka Ce: Wannan mujallar ta bayyana dalilan da suka nuna cewa an rubuta Littafi Mai Tsarki ne don mu fahimta. Ta kuma ambata abubuwa da za su iya taimaka mana mu fahimci Littafi Mai Tsarki.

HASUMIYAR TSARO (bangon baya)

Tambaya: Zan so in san ra’ayinka a kan wannan tambayar. [Ka karanta tambaya ta farko.] Wasu mutane sun yi imani cewa ba zai yiwu mu san Allah ba domin ya yi nisa da mu ainun. Mene ne ra’ayinka?

Nassi: 1Ti 2:3, 4

Abin da Za Ka Ce: Wannan talifin ya tattauna abin da Littafi Mai Tsarki ya ce a kan wannan batun. Zai yi kyau idan ka karanta shi. Bayan haka, za mu tattauna a wani lokaci.

ALBISHIRI DAGA ALLAH!

Abin da Za Ka Ce: Na zo ne in gaya maka game da nazarin Littafi Mai Tsarki da muke yi kyauta. Wannan ƙasidar ta nuna wurin da za ka sami amsoshin tambayoyi masu muhimmanci na rayuwa a cikin Littafi Mai Tsarki.

Tambaya: Ka taɓa karanta Littafi Mai Tsarki? Bari in nuna maka yadda wannan ƙasidar take da sauƙi. [Ku tattauna tambaya ta 1 a darasi na 2.]

Nassi: R. Yoh 4:11

KA RUBUTA TAKA GABATARWA

Ku yi amfani da fasalin da ke baya don rubuta taku gabatarwar wa’azi.