Yesu ya ba da misalai da yawa don ya nuna cewa sa kanmu ko kuma wasu tuntuɓe ba ƙaramin abu ba ne.

18:6, 7

  • Sa mutum “tuntuɓe” yana nufin yin wasu abubuwan da za su sa shi ya yi abin da bai kamata ba ko kuma ya yi zunubi

  • Gwamma a rataye wa mutum babban dutse a wuyansa kuma a jefa shi cikin teku da ya sa wani tuntuɓe

Babban dutse

18:8, 9

  • Yesu ya gaya wa mabiyansa su yanke hannunsu ko kuma cire idanunsu idan suna sa su tuntuɓe

  • Gwamma mutum ya rabu da waɗannan abubuwan kuma ya shiga Mulkin Allah, da ya zama da su kuma a halaka shi gabaki ɗaya

Mene ne nake yi da zai iya sa wasu tuntuɓe, kuma ta yaya zan guji sa kaina da kuma wasu yin tuntuɓe?