Bege yana kamar ƙugiya da ke riƙe jirgin ruwa. (Ibr 6:19) Yana taimaka mana mu ci gaba da bauta wa Jehobah sa’ad da muke fuskantar ƙalubale. (1Ti 1:18, 19) Ƙalubalen sun ƙunshi kurakuren da muka yi da ciwon da ya ƙi warkewa da rasuwa da takaici da hasarar dukiya ko kuma wani abu da zai iya shafar ibadarmu ga Jehobah.

Bege da kuma bangaskiya za su taimaka mana mu yi ɗokin ladar da Allah ya yi alkawarinta. (2Ko 4:16-18; Ibr 11:13, 26, 27) Saboda da haka, ko da muna da begen yin rayuwa a sama ko a duniya, wajibi ne mu riƙa bimbini a kan albarkar da aka yi alkawarinta a Kalmar Allah. Hakan zai taimaka mana mu jimre da jarrabawar da za mu fuskanta.1Bi 1:6, 7.

KU KALLI BIDIYON NAN KU RIƘA MURNA CIKIN BEGE, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Me ya sa ya kamata mu yi koyi da misalin Musa?

  • Wane hakki ne magidanta suke da shi?

  • Waɗanne batutuwa ne za ku iya tattaunawa a Ibadarku ta Iyali?

  • Ta yaya bege zai taimaka maka ka jimre da jarrabawa?

  • Mene ne kake begen gani a nan gaba?