Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

 RAYUWAR KIRISTA

Ku Yi Amfani da Littattafanmu Yadda Ya Dace

Ku Yi Amfani da Littattafanmu Yadda Ya Dace

Yesu ya ce: “Kyauta kuka karɓa, sai ku bayar kyauta.” (Mt 10:8) Muna bin wannan umurnin ta wajen ba mutane Littafi Mai Tsarki da kuma littattafanmu kyauta. (2Ko 2:17) Amma waɗannan littattafan suna koyar da gaskiya game da Allah. Kuma ana aiki tuƙuru da kashe kuɗi sosai wajen buga littattafan nan da kuma tura su zuwa ikilisiyoyi a faɗin duniya. Saboda haka, zai dace mu riƙa ɗaukan littattafan da muke bukata kawai.

Ku mai da hankali sosai sa’ad da kuke ba mutane littattafai, har sa’ad da kuke wa’azi da amalanke. (Mt 7:6) Maimakon kawai ku riƙa ba mutanen da suke wucewa mujalla, ku tattauna da su don ku san ko suna so su saurare ku. Shin za ka iya amsa e ga ɗaya daga cikin tambayoyin da ke akwatin nan? Idan ba ka san ko wani yana son abin da kuke tattaunawa ba, za ka iya ba shi warƙa. Ko da yake, za ka iya ba shi littattafanmu idan ya ce yana so.Mis 3:27, 28.