Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafin Taro Don Rayuwa Ta Kirista da Hidimarmu  |  fabrairu 2017

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ISHAYA 52-57

Yesu Ya Sha Azaba Domin Mu

Yesu Ya Sha Azaba Domin Mu

“Muka raina shi, muka ƙi shi . . . Mu kuwa muna tsammani wahalarsa hukunci ne Allah yake yi masa”

53:3-5

  • An rena Yesu kuma an zarge shi da yin saɓo. Wasu sun ce Jehobah yana masa horo ne kuma hakan na kamar ya daura masa cuta mai tsanani

“Ubangiji ya nufa a ƙuje shi; . . . nufin Ubangiji kuma za ya yi albarka a cikin hannunsa”

53:10

  • Babu shakka, Jehobah ya yi baƙin ciki sa’ad da aka kashe Ɗansa. Amma ya yi farin cikin ganin amincin Yesu. Mutuwar Yesu ta ba da amsa ga zargin da Shaiɗan ya yi game da amincin bayin Jehobah kuma ya kawo albarka ga mutanen da suka tuba. Don haka, mutuwarsa ta taimaka wajen cim ma “nufin” Jehobah