Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafin Taro Don Rayuwa Ta Kirista da Hidimarmu  |  fabrairu 2016

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ESTHER 1-5

Esther Ta Kare Mutanen Allah

Esther Ta Kare Mutanen Allah

Esther ta nuna bangaskiya da ƙarfin hali a lokacin da take kāre mutanen Allah

  • Za a iya kashe mutum idan ya je gaban sarki ba tare da izini ba. Kuma ba a gayyaci Esther ba har na tsawon kwana 30

  • Sarki Ahasuerus, wanda ake kira Xerxes na Ɗaya, mai zafin hali ne sosai. Akwai lokacin da ya sa a tsare wani mutum kashi biyu don ya koya wa wasu darasi. Kuma a lokacin da sarauniya Vashti ta yi masa rashin biyayya, ya sauƙe ta daga matsayinta

  • Esther ta gaya masa cewa ita Bayahudiya ce kuma amininsa ya yaudare shi