Akwai hanyoyi da dama a ƙungiyar Jehobah da matasa za su iya faɗaɗa hidimarsu. Ka kalli bidiyon nan Rayuwa Mafi Inganci don ka ga yadda Cameron ta yi amfani da ƙuruciyarta a hanyar da ta dace. Sai ka yi ƙoƙarin amsa tambayoyin da ke ƙasa. (Ka shiga jw.org/ha ƙarƙashin KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI > MATASA.)

  • Mene ne Cameron ta fi ɗauka wa da muhimmanci a rayuwarta?

  • Yaushe ta tsai da shawarar faɗaɗa hidimarta kuma ta yaya ta yi hakan?

  • Yaya ta yi shiri don ta yi hidima a inda ake da bukatar masu shela a wata ƙasa?

  • Waɗanne ƙalubale ne Cameron ta fuskanta yayin da take hidima a wata ƙasa?

  • Me ya sa zai kasance da albarka mu yi hidima a wani wuri da ba mu taɓa hidima ba?

  • Ta yaya Allah ya albarkaci Cameron?

  • Me ya sa hidimar Jehobah ce kaɗai take sa mutum ya yi rayuwa mafi inganci?

  • Waɗanne maƙasudai ne matasa za su iya kafawa a ƙungiyar Jehobah?