Mene ne za mu koya daga yadda aka warware matsalar nan?

15:​1, 2—Mu kasance da sauƙin kai da kuma haƙuri. Maimakon Bulus da Barnaba su sasanta matsalar da kansu, sun nemi ja-gora daga ƙungiyar Jehobah.

15:​28, 29—Mu gaskata da ƙungiyar Jehobah. ’Yan’uwan da ke ikilisiyar sun gaskata cewa Jehobah zai yi amfani da ruhu mai tsarki da kuma Yesu Kristi don ya warware matsalar.

16:​4, 5—Mu yi biyayya. Ikilisiyoyin sun ci gaba da ƙaruwa kuma bangaskiyarsu ta ƙara yin ƙarfi domin sun bi umurnin hukumar da ke kula da ayyukansu a lokacin.