Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

 RAYUWAR KIRISTA

Ku Ratsa Zuciya da Littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Kaunar Allah”

Ku Ratsa Zuciya da Littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Kaunar Allah”

MUHIMMANCINSA: Idan muna so mutane su bauta wa Jehobah yadda ya dace, wajibi ne su koyi ƙa’idodinsa kuma su bi su. (Ish 2:3, 4) Muna amfani da littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah” wajen yin nazari da ɗalibanmu bayan mun kammala nazarin littafi na farko da su. Muna haka don mu taimaka musu su san yadda za su yi amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. (Ibr 5:14) Zai dace mu ratsa zuciyarsu don su iya gyara halayensu.—Ro 6:17.

YADDA ZA MU CIM MA HAKAN:

  • Ka san yanayin ɗalibinka sosai don ka gane yadda za ka yi shiri don nazarin. Ka shirya wasu tambayoyin da za ka yi masa don ka san ra’ayinsa game da batun da kuke tattaunawa.—Mis 20:5; be-E 259

  • Ka yi amfani da akwatunan da ke littafin wajen taimaka wa ɗalibin ya ga muhimmancin bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki

  • Idan batu ne da babu wata doka a kai, ka bar shi ya yanke wa kansa shawara.—Ga 6:5

  • Ka yi ƙoƙarin sanin ko ɗalibinka yana bukatar taimako wajen bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Ka ƙarfafa shi ya san cewa ya kamata ƙaunarsa ga Jehobah ta motsa shi ya gyara halayensa.Mis 27:11; Yoh 14:31