Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Ana nazarin Littafi Mai Tsarki a ƙasar Chile

LITTAFIN TARO DON RAYUWA TA KIRISTA DA HIDIMARMU Disamba 2016

Gabatarwa

Yadda za a iya ba da mujallar Awake! da kuma koya wa mutane gaskiya game da dalilin da ya sa muke shan wahala. Ka yi amfani da misalan nan don ka rubuta taka gabatarwar.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

“Ku Zo, Mu Hau Zuwa Dutsen Ubangiji”

Annabi Ishaya ya kwatanta yadda za a mayar da kayan yaki su zama na noma kuma hakan ya nuna cewa mutanen Jehobah za su kasance da salama. (Ishaya 2:4)

RAYUWAR KIRISTA

Ku Ratsa Zuciya da Littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Kaunar Allah”

Littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Kaunar Allah” yana taimaka wa daliban Littafi Mai Tsarki su san yadda za su yi amfani da ka’idodin Littafi Mai Tsarki.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Almasihu Ya Cika Annabci

Ishaya ya annabta cewa Almasihu zai yi wa’azi a ketaren Galili. Yesu ya cika wannan annabcin sa’ad da ya je wurare dabam-dabam don ya yi wa’azin bishara.

RAYUWAR KIRISTA

“Ga Ni; Ka Aike Ni!”

Ta yaya za mu iya yin koyi da halin sadaukarwa da kuma bangaskiyar da Ishaya ya kasance da shi? Ka koyi daga wata iyali da suka kaura zuwa inda ake bukatar masu shela sosai.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Sanin Jehobah Zai Cika Duniya

Ta yaya annabcin da Ishaya ya yi game da al’janna a nan duniya ya cika a zamanin dā da namu da kuma zai cika a nan gaba?

RAYUWAR KIRISTA

Koyarwar Allah Tana Sa Mu Daina Nuna Wariya

Wasu mutane biyu da a dā maƙiya ne sun zama ‘yan’uwa—hakika koyarwar Allah tana da aiko sosai.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Yin Wulakanci da Ikonmu Zai Sa Mu Rasa Gatanmu

Yaya ya kamata Shebna ya yi amfani da ikonsa? Me ya sa Jehobah ya ba wa Eliakim matsayinsa?