Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafin Taro Don Rayuwa Ta Kirista da Hidimarmu  |  Agusta 2017

 RAYUWAR KIRISTA

Ku Kasance da Halaye Masu Kyau​—Bangaskiya

Ku Kasance da Halaye Masu Kyau​—Bangaskiya

ME YA SA TAKE DA MUHIMMANCI:

  • Wajibi ne mu kasance da bangaskiya idan muna so mu faranta wa Allah rai.​—Ibr 11:6

  • Idan muka gaskata da alkawuran Allah, za mu jimre jarrabawa.​—1Bi 1:6, 7

  • Za mu iya yin zunubi idan ba mu da bangaskiya.​—Ibr 3:12, 13

YADDA ZA KA KASANCE DA HALIN:

  • Ka roƙi Allah ya sa ka kasance da bangaskiya sosai.​—Lu 11:9, 13; Ga 5:22

  • Ka karanta Kalmar Allah kuma ka yi bimbini a kai.​—Ro 10:17; 1Ti 4:15

  • Ka riƙa tarayya da mutane masu bangaskiya sosai.​—Ro 1:11, 12

Ta yaya zan ƙarfafa bangaskiyata da ta iyalina?

KU KALLI BIDIYON NAN KU KOYI HALAYEN DA ZA SU ƘARFAFA AMINCINKU​BANGASKIYA, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Me ake nufin da “bangaskiya marar riya,” wato ta ƙwarai? (1Ti 1:5)

  • Idan muna son bangaskiyarmu ta yi ƙarfi, mene ne ya kamata mu guje wa?

  • Me ya sa muke bukatar bangaskiya a lokacin ƙunci mai girma? (Ibr 10:39)