Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafin Taro Don Rayuwa Ta Kirista da Hidimarmu  |  Agusta 2017

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | EZEKIYEL 32-34

Hakkin da Mai Tsaro Yake da Shi

Hakkin da Mai Tsaro Yake da Shi

Masu tsaro suna tsayawa a kan ganuwar birni don su sanar da mutanen da ke cikin gari game da haɗarin da ke tafe. Jehobah ya ba Ezekiyel matsayin “mai-tsaro ga gidan Isra’ila.”

  • 33:7

    Ezekiyel ya gaya wa Isra’ilawa cewa za a hukunta su idan ba su daina mugunta ba

    Wane saƙon Jehobah ne muke yin shelarsa a yau?

  • 33:9, 14-16

    Ezekiyel zai iya ceton ransa da kuma na mutane idan ya yi shelar saƙon

    Me ya kamata ya motsa mu mu yi shelar saƙon da Jehobah ya ba mu da gaggawa?