Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Ka Zabi Yare Hausa

Wasu ’yan’uwa suna ba da ƙasidar nan Albishiri Daga Allah! a ƙasar Azerbaijan

LITTAFIN TARO DON RAYUWA TA KIRISTA DA HIDIMARMU Agusta 2017

Gabatarwa

Yadda za a iya ba da mujallar Awake! da kuma koyar da gaskiya game da Mulkin Allah. Ka yi amfani da misalan nan don ka rubuta taka gabatarwar.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Jehobah Ya Albarkaci Kasar da Ba Ta Bauta Masa

Jehobah ya albarkaci kasar Babila bayan sun yi shekara 13 suna yaki da mutanen Tyre. Ta yaya ya saka musu don aikin da suke yi masa?

RAYUWAR KIRISTA

Ku Kasance da Halaye Masu Kyau​—Saukin Kai

Me ya sa saukin kai yake da muhimmanci? Ta yaya za mu kasance da saukin kai? Ta yaya yin addu’a da kuma yin koyi da misalin Yesu zai taimaka mana mu nuna saukin kai?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Hakkin da Mai Tsaro Yake da Shi

Masu tsaro suna da aiki mai muhimmanci na gaya wa mutane hadarin da ke tafe. Mene ne Jehobah yake nufi sa’ad da ya nada Ezekiyel a matsayin mai tsaro ga Isra’ilawa?

RAYUWAR KIRISTA

Ku Kasance da Halaye Masu Kyau​—Karfin Hali

Me ya sa ya kamata mu daina jin tsoron mutum? Ta yaya yin bimbini da addu’a da kuma dogara ga Jehobah yake taimaka mana mu kasance da karfin hali?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Za a Halaka Gog na Magog Nan Ba da Dadewa Ba

Littafi Mai Tsarki ya bayyana abubuwan da za su faru kafin a halaka Gog na Magog da bayan an halaka su.

RAYUWAR KIRISTA

Ku Kasance da Halaye Masu Kyau​—Bangaskiya

Ya kamata mu kasance da bangaskiya mai karfi kamar Ibrahim sa’ad da muke fuskantar matsaloli. Ta yaya za mu kasance da bangaskiya mai karfi da kuma aminci?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Yadda Wahayin Ezekiyel Game da Haikali Ya Shafe Ka

Wahayin haikalin da Ezekiyel ya gani ya tuna mana cewa Jehobah yana son ibada mai tsabta. Ta yaya wannan wahayin zai iya motsa mu?

RAYUWAR KIRISTA

Yaushe Ne Zan Sake Yin Hidimar Majagaba Na Dan Lokaci?

Hanya daya da za mu sadaukar da kanmu ita ce yin hidimar majagaba na dan lokaci. Za ka iya kyautata hidimarka a wannan hanyar?