Mutane a faɗin duniya suna bukatar ta’aziya. (M. Wa 4:1) Za mu rarraba Hasumiyar Tsaro ga mutane a watan Satumba, kuma za mu tattauna game da ta’aziya. Ka saka hannu don a rarraba wannan mujallar a duk faɗin duniya. Amma, tun da yake mun fi so mu tattauna da mutane don mu ƙarfafa su, ba zai dace mu ajiye mujallunmu a ƙofar gidajen mutanen da ba sa gida ba.

ABIN DA ZA KA CE

“Ba wanda ba ya bukatar ta’aziya. Amma ta yaya za mu iya samun ta’aziya? [Karanta 2 Korintiyawa 1:3, 4.] Wannan mujallar Hasumiyar Tsaro ta tattauna yadda Allah yake ta’azantar da mu.”

Idan mutumin yana son saƙonmu kuma ya karɓi mujallar, . . .

KA NUNA BIDIYON ME YA SA ZAI DACE MU YI NAZARIN LITTAFI MAI TSARKI?

Kuma ka ce za ka dawo don ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi.

KA YI SHIRIN KOMA ZIYARA

Sai ka ce za ka dawo don ku tattauna tambayar nan “Me ya sa Allah ya ƙyale mugunta da wahala?