Koma ka ga abin da ke ciki

Koma secondary menu

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shaidun Jehobah

Hausa

Littafin Taro Don Rayuwa Ta Kirista da Hidimarmu  |  Agusta 2016

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ZABURA 87-91

Ka Kasance Cikin Mabuyan Madaukaki

Ka Kasance Cikin Mabuyan Madaukaki

“Maɓuyan” Jehobah yana kāre dangantakarmu da shi

91:1, 2, 9-14

  • Idan muna so mu kasance cikin maɓuyan Jehobah a yau, dole ne mu keɓe kanmu kuma mu yi baftisma

  • Mutanen da ba su dogara ga Allah ba ba su san wannan maɓuyan ba

  • Mutanen da ke maɓuyan Jehobah ba sa barin kome ko kuma kowa ya raunana imaninsu da kuma ƙaunarsu ga Allah

‘Mai farautanʼ yana ƙoƙarin ɗana mana tarko

91:3

  • Tsuntsaye suna da wayo da kuma wuyan kamawa

  • Masu farautar tsuntsaye suna lura da tsuntsaye sosai don su san yadda za su kama su

  • Shaiɗan, wanda shi ne “mai-farauta,” yana neman dabaru iri-iri da zai yi amfani da su wajen sa bayin Jehobah su daina bauta masa

Dabaru huɗu da Shaiɗan yake amfani da su:

  • Tsoron Mutum

  • Kayan Duniya

  • Nishaɗi Marar Kyau

  • Saɓani