MUHIMMANCINSA: Idan ɗaliban da muke nazari da su suna son Jehobah ya amince da su, wajibi ne su keɓe kansu kuma su yi baftisma. (1Bi 3:21) Idan suka yi rayuwar da ta jitu da alkawarin da suka yi, Jehobah zai kāre su a hidimar da suke yi. (Za 91:1, 2) Kirista yana keɓe kai ga Jehobah ne ba ga wani mutum ko aiki ko kuma wata ƙungiya ba. Saboda haka, ɗalibanmu suna bukatar su san yadda za su ƙaunaci Jehobah kuma su riƙa nuna godiya.—Ro 14:7, 8.

YADDA ZA MU CIM MA HAKAN:

  • A lokacin da kuke nazarin, ka taimaka masa ya ga yadda abin da kuke tattaunawa ya nuna wasu halayen Jehobah. Ka koya masa muhimmancin karanta Littafi Mai Tsarki kullum da kuma yin addu’a “ba fasawa.”—1Ta 5:17; Yaƙ 4:8

  • Ka ƙarfafa ɗalibinka ya kafa maƙasudin keɓe kai ga Jehobah da kuma yin baftisma. Ƙari ga haka, za ka iya taimaka masa ya soma yin kalami a taro da kuma yi wa maƙwabta da abokansa wa’azi. Kuma ka tuna cewa Jehobah ba ya tilasta mana mu bauta masa. Shi ya sa keɓe kai ga Jehobah shawara ce da ɗalibin zai yanke wa kansa.—K. Sh 30:19, 20

  • Ka taimaka wa ɗalibinka ya yi wasu canje-canje don ya faranta wa Jehobah rai kuma ya cancanci yin baftisma. (Mis 27:11) Da yake wasu halayen da ɗalibinmu yake da su sun zama masa jiki, yana bukatar lokaci da taimako sosai don ya daina yin su. (Afi 4:22-24) Ka nuna wa ɗalibin talifofin nan “Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane” da ake wallafawa a Hasumiyar Tsaro

  • Ka gaya masa abubuwa masu kyau da ka shaida a hidimarka ga Jehobah.—Ish 48:17, 18