10:13

Jehobah zai iya kawar mana jarabar da muke fuskanta. Amma, a yawancin lokuta yakan buɗe mana “hanyar tsira” ta wurin tanada mana abubuwan da za su taimaka mana mu jimre.

  • Zai iya yin amfani da Kalmarsa da ruhunsa da littattafai da kuma bidiyoyi don ya taimaka mana da kuma ƙarfafa mu mu yi tunani da kyau.​—Mt 24:45; Yoh 14:16; Ro 15:4

  • Zai iya ba mu ruhunsa mai tsarki don ya tuna mana ayoyi da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka mana mu san irin shawarar da ya kamata mu yanke.​—Yoh 14:26

  • Zai iya yin amfani da mala’ikunsa don ya taimaka mana.​—Ibr 1:14

  • Zai iya yin amfani da ’yan’uwanmu Kiristoci don ya taimaka mana.​—Kol 4:11